23 Satumba 2019 - 04:27
​Sojojin Sudan Sun Fara Janyewa Daga Kasar Yemen

Wani Gungun Sojin kasar Sudan dake cikin kawancen Saudiya a kasar Yemen sun fice daga yammacin kasar zuwa sansanin Sojin Asab na kasar Eritrea

(ABNA24.com) Wani Gungun Sojin kasar Sudan dake cikin kawancen Saudiya a kasar Yemen sun fice daga yammacin kasar zuwa sansanin Sojin Asab na kasar Eritrea

Kamfanin dillancin labaran Irna ya ruwaito cewa a safiyar wannan lahadi, wani gungu na sojojin kasar Sudan dake cikin kawancen saudiya sun fara ficewa daga yammacin kasar ta Yemen, inda suka nufi sansanin sojoji na Asab dake kasar Eritrea.

Gwamnatin kasar Sudan dai ta karbi kudi daga wajen hukomomin saudiya da hadadiyar daular larabawa wajen aikewa da sojojinsu zuwa kasar Sudan.

Al'ummar kasar Sudan dai sun jima suna gudanar da zanga-zanga na nuna adawa da tura dakarunsu zuwa kasar Yemen, tare da neman kasar ta dawo da dakarun kasar gida.

Tun a watan Maris na shekarar 2015 ne kasar Saudiya tare da hadaddiyar daular larabawa bisa goyon bayan Amurka ta kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar kasar Yemen tare da killace kasar ta sama da kasa da kuma ruwa.

Ya zuwa yanzu kuma, hare-haren wuce gona da irin da kawancen Saudiya ke kaiwa kasar ta yemen ya yi sanadiyar mutuwar yamaniyawa sama da dubu 16 da kuma jikkata wasu dubai na daban tare kuma da raba wasu milyoyin jama’a da mahalinsu.



/129